Deby ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou ya kai masa ziyara a birnin Ndjamena.
A cewar Mr Deby, sun san inda Shekau ya boye.
"Idan Abubakar Shekau na son kansa da lafiya, to ya mika wuya, mun san inda yake. Idan bai mika wuya ba, makomarsa za ta zama iri daya da sauran mabiyansa," in ji shugaba Deby.
Rikicin Boko Haram wanda aka soma a Najeriya a yanzu ya shiga makwabtan kasashe kamarsu Chadi da Kamaru da kuma Nijar.
Mutane fiye da 13,000 ne suka rasu tun da aka soma rikicin Boko Haram a Najeriya. ABNA